iconznigeria Results Translation

Transcription

iconznigeria Results Translation
SAKAMAKON BINCIKEN DA ICONZ TAYI A KACHIA
GRAZING RESERVE (LADDUGA) DA SHAWARWARI GA
MAKIYAYA A KAN CUTUTTUKAN
NATIONAL VETERINARY RESEARCH
INSTITUTE, VOM, NIGERIA
MIYETTI
SAKAMAKO DA SHAWARWARI AKAN BINCIKEN DA
ICONZ TAYI A KACHIA GRAZING RESERVE
(LADDUGA)
ALHAMDU-LIL-LAHI
MENENE ICONZ?
Iconz kalma ce da ta kunshi kalmomi biyar a dunkule. Tana nufin
gamammen shiri don tinkaran cututtuka masu yaduwa tsakanin
dabbobi da mutane.
Tarayyan kasashen Turai, wato European Union (EU) ke tallafawa
wannan shirin.
Z tana matsayin 'zoonoses' a turance
Tana nufin cututtuka da mutane kan iya samu daga dabbobi ko
kamuwa da su daga dabbobi ana kiran su “ zoonoses” a turance.
Misalen wadannan cututtukan sun hada da bakkale da tari,
cututtuka Kaman sammore,goli da hanta basa yaduwa tsakanin
dabbobi da mutane, don haka mutane basa kamuwa da su daga
dabbobi.
C tana matsayin 'control' a turance
Tana nufin hana yaduwar cututtuka. Sanin cewa mutane na iya
kamuwa da wasu cututtuka daga dabbobi, na da muhimmanci don
kula da lafiya. Kula da lafiyan dabbobi don kare su daga cututtuka,
musamman ma wadanda ke yaduwa tsakanin dabbobi da mutane
ya zama dole. In dabbobi na da koshin lafiya, sun fi bada
riba:(madara, nama, kwai da haihuwa akai akai), kuma wadannan
1
14
ii.
iii.
iv.
kindirmo, awara da sauran su. Haka na kashe
duk wasu cututtuka, a tabbata madara yayi
minti biyar yana tafasa.
Ka tabbata ka sanya kariyar hannane kamin
taimakawa dabba wajen haihuwa, ko yayin
tattara abinda dabba ta barar.
Kada a ci ko a sayar da huhun da ke dauke da
gudaji. Wannan na dauke da kwayoyin ciwon
tari. A yanke, a binne ko a kone.
Har kullum, a tabbata an dafa nama sosai. A
guji cin naman da bai dafu ko gasu sosai
ba.wuta ko zafi na kashe kwayoyin ciwo.
GODIYA
-
-
-
Muna mika godiya ga dukkan al'umman Ladduga
saboda karbuwan da muka samu daga garesu.
Muna mika godiya na musamman ga dukkan gidajen
da muka yi aiki dasu. Da Hakimin Ladduga da
sauran sarakunan.
Muna godewa Sulaiman da Isma'il wadanda suka
kasance jagororin mu. Da Salisu da Adamu wadanda
suma sun taimaka sosai.
Dr. Jamo wanda ya taimaka sosai kuma ya bada
masauki don wannan aiki.Muna cewa mun gode
sosai, Allah ya bamu lafiya da zama lafiya da mu da
dabbobin mu a Ladduga da ma Najeriya gaba daya.
13
ribace ribacen sukan zama amintattu don ana da tabbacin lafiyan
dabbobin. Bayan tabbatar da lafiyan dabbobin mu, ya zama tilas
muyi ta sarrafa ababan amfani da muke samu daga dabbobi ta
hanyan da bazasu cutar da mu ba. Misali tafasa madara, dafa nama
sosai da sauransu. Ta haka ne kawai zamu samu tabbatacciyar
kariya daga cututtukan da muka ambata a baya. Wadannan
abubuwa biyu (kare dabbobi daga cututtuka, da kuma tsare
mutane daga kamuwa da cututtuka daga dabbobi) sune hanyoyin
kariya daga cututtuka a mutane da dabbobi
I tana matsayin 'integrated' a turance
Tana nufin zamar da abu kammalalle ta hanyar kawo dukkan
bangarorin shi a wuri guda. Yana daga cikin tsarin aikin ICONZ in
za ta yi bincike, ta tabbatar ta yi la'akari da abubuwa masu yawa,
misali, ta yi bincike akan cututtuka daban daban a dabbobi daban
daban, har ma da mutane. Hakan na taimaka wajen gano abin da ke
jawo matsala a lafiyan dabbobi da mutane a inda suke, imma
Gunduma ce, ko Karamar Hukuma, ko ma Jiha gaba daya. Kamar
lemu ne, imba an tsaga aka kuma bare shiba, baza a gane abun da ta
kunsa ba.
ABUBUWAN DA MUKA YI A LADDUGA TSAKANIN
2010 ZUWA 2012
- Shekaru biyu da suka gabata (Dec 2010 Oct 2012) al'uman
Ladduga sun karbi bakoncin wata tawagan kwararru da ta
kunshi masana daga hukumar binciken cututtukan dabbobi
wato N.V.R.I Vom, masana daga Jami'ar Edinburgh (UK) ta
Turai da kuma masana daga Jami'ar Navarra (Spain) ta
2
Faransa. Wannan tawagar ta zo Ladduga musamman don ta
gudanar da bincike akan cututtuka kamar haka:
-Sammore a shanu, tumaki da awaki.
- Bakkale a shanu, tumaki, awaki da mutane.
- Ciwon tari a shanu da kuma
- Hanta da goli a shanu.
- Bayan bincike akan wadannan cututtukan, tawagar ta yi
kokari wajen fahimtan mutanen Ladduga, musamman
abinda ya shafi al'adunsu da al'amuran yau da kullum.
Sanin haka zai taimaka sosai wajen bada shawarwari
nagartattu akan kiwon lafiya. Don haka kuka ga tawagar
tayi ta yin tambayoyi wa maza da mata, yara da manya, har
ma da mahauta.
- Abin jan hankali anan, mutanen Ladduga su sani cewa
binciken da wannan tawaga ta ICONZ ta iya gano bayane
akan kadan daga cikin cututtukan dabbobi. Da yawa yawa
ba'a tabo su ba. cututtuka kamar huhu, kirchi, sefa da
sauran su, baza'a iya cewa komai a kan su ba. Don haka,
shawarwarin da wannan shirin zata bayar na shafan
sammore, bakkale, tari, goli, da kuma hanta kawai.
-
Kamin wadannan shawarwarin, ga sakamakon binciken
cultuttukan da akayi a lissafe
3
yaduwar tari:I.
A guji seyan dabba a kawo cikin garke nan
take.
ii.
A guji hada shanu da wadanda sun taba ciwon
tari.
iii.
A gaggauta fidda dabba mai nuna halamar tari
(ramewa, tari da kumburin wuya) daga garke.
YADDA ZAKA KARE KANKA DA IYALENKA
DAGA DAUKAN BAKKALE DA TARI DAGA
DABBOBI.
Kamar yadda muka bayyana a farko, mutum na iya
kamuwa da bakkale ko tari daga dabbobin sa kamar
haka:i.
Shan danyan madaran dabba mai dauke da
ciwon bakkale ko tari.
ii.
Taimakawa dabba mai bakkale yayin haihuwa
ba tare da sanya kariyar hannaye ba.
iii. Daukar abun da dabba ta barar ba tare da sanya
kariyar hannaye ba.
iv.
Cin huhun dabba mai dauke da tari
Zaka iya gane ciwon tari a yankakken dabba. Zaka ga
wasu gudaji - gudaji a kan huhun dabbar. In aka
tsaga wadannan gudaji gudaji, za'aga wani farin abu
mai kamar alli a ciki.
Ka kare kan ka da iyalenka daga wadannan
cututtuka kamar haka:
i.
A tafasa madara kamin sha ko sarrafawa zuwa
12
(i)
(ii)
(iii)
(iv)
(v)
A ware dabbobi da suka yi kusan haihuwa daga
garke. Bayan haihuwa a ci gaba da kebe su na tsawon
mako uku zuwa hudu.
In dabba tayi bari, a tattara duk abin da ta barar a toni
rami a binne ko a kone. Kar a bawa karnuka.
A yi amfani da abin kare hannaye wajen tattara abun
da dabba ya barar.
Duk dabban da ta bayyana tana da bakkale, a kaita
kasuwa don kada ta yada ciwon.
Yin bari a cikin farko na iya zama bakkale, haka
kumburi musamman a gwiwa da wasu gaba na nuna
halaman bakkale. A tattara duk ire iren su a kai
kasuwa.
HANA YADUWAN TARI
Ciwon tari yana kama dabba da mutum. Halamomin
tari basu bayyana a dabba da wuri, don haka duk abun
da za'ayi yakan zama a makare.
Halamomin tari a shanu sune:
Tari
Ramewa
Matsalar numfashi, sannan a wani sa'in akwai
kumburewan wuya.
Kasancewar halamomi na bayyana a makare, ba'a iya
hana yaduwar tar a dabbobi.
Abun farin ciki, bamu samu dabbobi masu ciwon tari
sosai a Ladduga ba.
Ayi amfani da wadannan hanyoyi don rage ko hana
11
:
Disease
Brucellosis
Bovine
tuberculosis
Fufulde
name
Period of
sampling
Bakale
June 2011 Cattle
October 2011 Sheep
Helminths
Bonostomum
phlebotomum
Cooperia pectinata
Oesophagostomum
radiatum
Strongyloides papillosus
Tricuris globulosa
Strongylus laryngeus
Paramphistomum cervi
Fasciola gigantica
Eimeria bovis
Schistosoma bovis
Moniezia benedeni
How many animals/ How many HH/
people are infected? herds are infected?
10/1963 = 0.5%
7/40 = 17.5%
2/717 = 0.3%
2/52 = 3.8%
Goat
717 (52
752 (52)
0%
0%
People
1124 (80)
0%
0%
Cattle
1944 (40)
103/1944 = 5.2%
29/40 = 72%
June 2011 Cattle
1982 (40)
278/1982 = 14%
34/40 = 85%
October 2011 Sheep
717 (52)
31/717 = 4.32%
ND2
Goats
752 (52)
24/752 = 3.09%
ND
June 2011
Trypanosomiasis Samore
(overall prevalence, cattle with 1 or
more of helminths below)
Number animals/
people sampled
(no. Hh1 Sampled)
1963 (40)
Tari
Disease
Species
Fufulde
name
Hanta/
Goli
Period of
sampling
Species
Number animals/
people sampled
(no. Hh1 Sampled)
June 2011
Cattle
1981 (40)
How many animals/ How many HH/
people are infected? herds are infected?
1332/1981 = 62.2%
39/40 = 97.5%
Goli
Goli
Goli
Goli
4/1981 = 0.2%
3/40 = 7.5%
145/1981 = 7.3%
296/1981 = 14.94%
19/40=47.5%
32/40 = 80%
Goli
Goli
Goli
Goli
Hanta
Goli
Goli
Goli
12/1981= 0.61%
237/1981 = 11.96%
0/1981 = 0%
850/1981 = 42.91%
106/1980 = 5.35%
353/1977 = 17.79%
3/1981 = 0.15%
1/1981=0.05%
4/40 = 10%
16/40 = 40%
0/40 = 0%
39/40=97.5%
25/40= 62.5%
36/40 = 90%
2/40 = 5%
1/40 = 2.5%
4
FADAKARWA DA SHAWARWARI GA MAKIYAYA AKAN
SAMMORE, KUDAN TSANDO, GOLI, HANTA,
BAKKALE DA KUMA TARI.
SAMORE:
Sammore ciwo ne wanda cizon kudan tsando ke
haddasa wa dabbobi (Shanu, Tumaki, Awaki,e.t.c).
Sammore kan iya shafan mutum ma.
ciwon na bayyana bayan kwayar ta shiga jinin dabba,
tare da hayayyafa.
halamomin ciwon a dabba sun hada da zazzabi,
tashin gashi, hawaye,ramewa,jemewar gashin
wutsiya sannan kuma in yayi tsanani, dabba yayi ta
cin kasa har ya mutu.
Sammore yafi kama shanu, amman tumaki da awaki
ma suna yin Sammore.
Binciken da muka yi a Ladduga ya nuna shanu da
yawa na fama da Sammore, amma tumaki da awaki
basu da wannan damuwar sosai.
Don haka, Shanu sun cancanci kariya daga sammore.
Sai a ringa yiwa dukkan garken shanu alluran
rigakafin Sammore, a kuma kare su daga tsando. Duk
da wadannan kariyan, ba'arasa kadan daga cikin
shanu masu kamuwa da sammore. In haka ya faru, to
sai ayi anfani da magani na musamman don jinya.
Tattaunawan da muka yi daku ya nuna kuna yin
abinda ya dace a kan sammore, amma shawarin mu
5
-
-
-
shiga. Wannan “Clostridium” shi yake haddasa kisa
ga dabban da ke da “hanta”.
Ma'aikatar binciken cututtukan dabbobi da ke VOM,
wato N.V.R.I na yin maganin rigakafin wannan
ciwon Clostridium, an fi sanin wannan magani da
HANTAVAC.
Don bawa dabbobin mu cikakken kariya sai a ringa
ba shanu da tumaki/awaki maganin duri da rigakafin
HANTAVAC.
Ana yin rigakafin hanta sau biyu a shekara, (Bazara
da kaka).
BAKKALE DA TARI
Bakkale da tari cututtuka ne masu addaban dabbobi
da mutane. Alhamdulilahi, anan Ladduga dai
bamuga wadannan matsalolin sosai ba. Shanu kadan
aka samu da bakkale da tari.
Abun murna, ko mutum daya ba'a samu da ciwon
bakkale ba. Wannan ya nuna ana kula sosai.
Shawarin mu anan kawai shine:
(a) A kula sosai kada dan kadan na dabbobi masu
matsalan nan su yada wa sauran.
(b) Mutane su yi hattara kada su kamu da cuttuttuka
(Bakkale da Tari) daga dabbobi marasa lafiya.
HANA YADUWAR BAKKALE
Wadannan hanyoyin zasu rage yaduwar bakkale
sosai.
10
-
ga karuwar kuda ko randa za'a shigo inda ke da kuda
sosai.
Anfi samun tsando kusa da manyan rafuka kamar
rafin Kaduna, inda ke da kurmuna da kuma gangare.
GOLI DA HANTA
Goli da hanta wasu tsutsotsi ne da ake samu a hanji da
hantan dabbobi masu matsalar. Shanu, tumaki da awaki duk
suna kamuwa da goli ko hanta.
Binciken da muka yi a Ladduga ya nuna shanu da
yawa na dauke da hanta da goli. Haka kuma
tattaunawan mu da mahautan Ladduga, sun gaya
mana sukanga wadannan tsutsotsi a hanji da hantan
dabbobin da aka yanka.
Abun farin ciki anan, akan iya magance goli da hanta
da magani daya.
Ayi wa dabbobi duri a farkon damina (watan shida)
da karshen damina (watan tara).
Ayi amfani da magani mai sinadarin Levamisole da
Oxyclozanide, misali KEPZAN.
Ana bawa babbar sa kwaya daya da rabi zuwa kwaya
biyu na Kepzan. Sai a budi bakin sa a sa kwayar
magani, a bida ruwa.
Kar a sha madaran san da aka bada Kepzan sai bayan
kwana daya.
Hanta da goli basu kashe dabba, amma kasancewar
su a hantan dabba kan yi wa hantan lahani ta inda
wata kwayar ciwo nau'in “Clostridium” ke samun
9
anan kawai, a ringa yin wa dukkan garke alluran
rigakafin sammore, a tabbatar ana bada dai-dai
yawan maganin da ya dace da girman dabba.
Shanun da basu da lafiya kuma, ayi amfani da
maganin jinya.
H A N YA N B A D A S H A N U K A R I YA D A G A
SAMMORE:
Ayi amfani da Samorin a farkon bazara (watan Biyar
zuwa Shida), ko kamin a kaura zuwa wuraren dake
da tsando.haka kuma kamin dawowa zuwa Ladduga.
A tabbatar an bada magani bisa girman dabba, domin
in magani ya kasa, ya kan iya jawowar bijirewar
kwayar sammore (resistance). Aguji yin alluran
samorin a wuya musamman in Shanun noma ne.
Samorin na bada shanu kariya na wata uku, amma a
nau'in sammore mai wuyan sha'ani, kariyan baya kai
wata uku.
YADDA AKE HADA SAMORIN DA KUMA YIN
ALLURA:
Kayi amfani da ruwan da aka tafasa kuma ya huce
wajen hada samorin. Ka gwada ruwa lamba hamsin
ko dari wato allura biyar ko goma (50mls, or
100mls), ka juye pakitin samorin mai nauyin giram
daya a ciki, ka jijjiga har sai magani ya narke gaba
6
-
-
Weight
of the animal
daya.
Ka huda samorin cikin tsoka (i/m) in an jika da lamba
hamsin ne, a bada babbar sa lamba biyar (5 mls), in
kuma da lamba dari aka jika, a bada lamba goma (10
mls) wa babbar sa.
In akwai wata dabba mara lafiya kuma ana kyautata
zato sammore ne, to sai ita a bata maileda.
-
2% Solution
0.6mg/kg
-
A bada babbar sa lamba goma sha daya zuwa sha uku
(11 13mls) bisa ga nauyin ta.
Shima maileda ana yin alluran a cikin tsoka(i/m).
Kar a sha madarar san da aka mata allura da maileda
har sai bayan kwana bakwai (7days).
Kar a biye maileda da samorin ko samorin da maileda
har sai bayan sati uku.
Kar ayi ajiyan hadadden maileda ko samorin, ayi
amfani da su da zaran an jika.
1mg/kg
50kg
1.25ml
2.5ml
100kg
2.50ml
5ml
150kg
3.75ml
7.5ml
200kg
5ml
10ml
250kg
6.25ml
12.5ml
300kg
7.50ml
15ml
350kg
8.75ml
17.5ml
400kg
10ml
20ml
KARE DABBOBI DAGA CIZON KUDAN TSANDO
Binciken da muka yi ya nuna babu tsando sosai a
Ladduga, amma lokacin kaura akan iya fada a
wuraren da ke da tsando sosai.
Akan iya tsere wa sammore in ana kauce wa
wadannan wurare. In ya zama tilas a ziyarci
wadannan wurare, to ayi amfani da magani na
musamman don kariya daga tsando.
Magani mai sinadarin Deltamethrin, misali
Vectocid na bada shanu kariya sosai.
YADDA AKE HADA MAILEDA
Kayi amfani da ruwan da aka tafasa kuma ya huce.
Ka jika karamin patikin maileda (2.36g) daya da
ruwa lamba goma sha biyar (15mls). Ajijjiga har sai
magani ya narke gaba daya kamin ayi wa shanu
allura.
7
YADDA AKE AMFANI DA VECTOCID
Ka zuba lamba daya (1ml) na vectocid a ruwa lita
daya, ka garwaya sosai. Kayi amfani da abin feshi na
hanu ka fesa wa ko wane sa babba lita daya zuwa uku
(13 litres) a wuraren da tsando suka fi cizo/zama a
jikin sa kamar karkashin ciki da kafafuwa.
Kayi amfani da wannan magani a duk lokacin da ka
8

Similar documents

Chapter 19 - Masjid Tucson

Chapter 19 - Masjid Tucson huhunci ne na Ubangijinka. *19:71 Kamar yadda bayanin shafi 11 ta gwada, za tayar da mu kafin ainihin zatin Allah ya bayyana ga kaunin sammarmu. Wannan shi ne zai kasance dandanawar Jahannama na zu...

More information