iconznigeria Results Translation
Transcription
iconznigeria Results Translation
SAKAMAKON BINCIKEN DA ICONZ TAYI A KACHIA GRAZING RESERVE (LADDUGA) DA SHAWARWARI GA MAKIYAYA A KAN CUTUTTUKAN NATIONAL VETERINARY RESEARCH INSTITUTE, VOM, NIGERIA MIYETTI SAKAMAKO DA SHAWARWARI AKAN BINCIKEN DA ICONZ TAYI A KACHIA GRAZING RESERVE (LADDUGA) ALHAMDU-LIL-LAHI MENENE ICONZ? Iconz kalma ce da ta kunshi kalmomi biyar a dunkule. Tana nufin gamammen shiri don tinkaran cututtuka masu yaduwa tsakanin dabbobi da mutane. Tarayyan kasashen Turai, wato European Union (EU) ke tallafawa wannan shirin. Z tana matsayin 'zoonoses' a turance Tana nufin cututtuka da mutane kan iya samu daga dabbobi ko kamuwa da su daga dabbobi ana kiran su “ zoonoses” a turance. Misalen wadannan cututtukan sun hada da bakkale da tari, cututtuka Kaman sammore,goli da hanta basa yaduwa tsakanin dabbobi da mutane, don haka mutane basa kamuwa da su daga dabbobi. C tana matsayin 'control' a turance Tana nufin hana yaduwar cututtuka. Sanin cewa mutane na iya kamuwa da wasu cututtuka daga dabbobi, na da muhimmanci don kula da lafiya. Kula da lafiyan dabbobi don kare su daga cututtuka, musamman ma wadanda ke yaduwa tsakanin dabbobi da mutane ya zama dole. In dabbobi na da koshin lafiya, sun fi bada riba:(madara, nama, kwai da haihuwa akai akai), kuma wadannan 1 14 ii. iii. iv. kindirmo, awara da sauran su. Haka na kashe duk wasu cututtuka, a tabbata madara yayi minti biyar yana tafasa. Ka tabbata ka sanya kariyar hannane kamin taimakawa dabba wajen haihuwa, ko yayin tattara abinda dabba ta barar. Kada a ci ko a sayar da huhun da ke dauke da gudaji. Wannan na dauke da kwayoyin ciwon tari. A yanke, a binne ko a kone. Har kullum, a tabbata an dafa nama sosai. A guji cin naman da bai dafu ko gasu sosai ba.wuta ko zafi na kashe kwayoyin ciwo. GODIYA - - - Muna mika godiya ga dukkan al'umman Ladduga saboda karbuwan da muka samu daga garesu. Muna mika godiya na musamman ga dukkan gidajen da muka yi aiki dasu. Da Hakimin Ladduga da sauran sarakunan. Muna godewa Sulaiman da Isma'il wadanda suka kasance jagororin mu. Da Salisu da Adamu wadanda suma sun taimaka sosai. Dr. Jamo wanda ya taimaka sosai kuma ya bada masauki don wannan aiki.Muna cewa mun gode sosai, Allah ya bamu lafiya da zama lafiya da mu da dabbobin mu a Ladduga da ma Najeriya gaba daya. 13 ribace ribacen sukan zama amintattu don ana da tabbacin lafiyan dabbobin. Bayan tabbatar da lafiyan dabbobin mu, ya zama tilas muyi ta sarrafa ababan amfani da muke samu daga dabbobi ta hanyan da bazasu cutar da mu ba. Misali tafasa madara, dafa nama sosai da sauransu. Ta haka ne kawai zamu samu tabbatacciyar kariya daga cututtukan da muka ambata a baya. Wadannan abubuwa biyu (kare dabbobi daga cututtuka, da kuma tsare mutane daga kamuwa da cututtuka daga dabbobi) sune hanyoyin kariya daga cututtuka a mutane da dabbobi I tana matsayin 'integrated' a turance Tana nufin zamar da abu kammalalle ta hanyar kawo dukkan bangarorin shi a wuri guda. Yana daga cikin tsarin aikin ICONZ in za ta yi bincike, ta tabbatar ta yi la'akari da abubuwa masu yawa, misali, ta yi bincike akan cututtuka daban daban a dabbobi daban daban, har ma da mutane. Hakan na taimaka wajen gano abin da ke jawo matsala a lafiyan dabbobi da mutane a inda suke, imma Gunduma ce, ko Karamar Hukuma, ko ma Jiha gaba daya. Kamar lemu ne, imba an tsaga aka kuma bare shiba, baza a gane abun da ta kunsa ba. ABUBUWAN DA MUKA YI A LADDUGA TSAKANIN 2010 ZUWA 2012 - Shekaru biyu da suka gabata (Dec 2010 Oct 2012) al'uman Ladduga sun karbi bakoncin wata tawagan kwararru da ta kunshi masana daga hukumar binciken cututtukan dabbobi wato N.V.R.I Vom, masana daga Jami'ar Edinburgh (UK) ta Turai da kuma masana daga Jami'ar Navarra (Spain) ta 2 Faransa. Wannan tawagar ta zo Ladduga musamman don ta gudanar da bincike akan cututtuka kamar haka: -Sammore a shanu, tumaki da awaki. - Bakkale a shanu, tumaki, awaki da mutane. - Ciwon tari a shanu da kuma - Hanta da goli a shanu. - Bayan bincike akan wadannan cututtukan, tawagar ta yi kokari wajen fahimtan mutanen Ladduga, musamman abinda ya shafi al'adunsu da al'amuran yau da kullum. Sanin haka zai taimaka sosai wajen bada shawarwari nagartattu akan kiwon lafiya. Don haka kuka ga tawagar tayi ta yin tambayoyi wa maza da mata, yara da manya, har ma da mahauta. - Abin jan hankali anan, mutanen Ladduga su sani cewa binciken da wannan tawaga ta ICONZ ta iya gano bayane akan kadan daga cikin cututtukan dabbobi. Da yawa yawa ba'a tabo su ba. cututtuka kamar huhu, kirchi, sefa da sauran su, baza'a iya cewa komai a kan su ba. Don haka, shawarwarin da wannan shirin zata bayar na shafan sammore, bakkale, tari, goli, da kuma hanta kawai. - Kamin wadannan shawarwarin, ga sakamakon binciken cultuttukan da akayi a lissafe 3 yaduwar tari:I. A guji seyan dabba a kawo cikin garke nan take. ii. A guji hada shanu da wadanda sun taba ciwon tari. iii. A gaggauta fidda dabba mai nuna halamar tari (ramewa, tari da kumburin wuya) daga garke. YADDA ZAKA KARE KANKA DA IYALENKA DAGA DAUKAN BAKKALE DA TARI DAGA DABBOBI. Kamar yadda muka bayyana a farko, mutum na iya kamuwa da bakkale ko tari daga dabbobin sa kamar haka:i. Shan danyan madaran dabba mai dauke da ciwon bakkale ko tari. ii. Taimakawa dabba mai bakkale yayin haihuwa ba tare da sanya kariyar hannaye ba. iii. Daukar abun da dabba ta barar ba tare da sanya kariyar hannaye ba. iv. Cin huhun dabba mai dauke da tari Zaka iya gane ciwon tari a yankakken dabba. Zaka ga wasu gudaji - gudaji a kan huhun dabbar. In aka tsaga wadannan gudaji gudaji, za'aga wani farin abu mai kamar alli a ciki. Ka kare kan ka da iyalenka daga wadannan cututtuka kamar haka: i. A tafasa madara kamin sha ko sarrafawa zuwa 12 (i) (ii) (iii) (iv) (v) A ware dabbobi da suka yi kusan haihuwa daga garke. Bayan haihuwa a ci gaba da kebe su na tsawon mako uku zuwa hudu. In dabba tayi bari, a tattara duk abin da ta barar a toni rami a binne ko a kone. Kar a bawa karnuka. A yi amfani da abin kare hannaye wajen tattara abun da dabba ya barar. Duk dabban da ta bayyana tana da bakkale, a kaita kasuwa don kada ta yada ciwon. Yin bari a cikin farko na iya zama bakkale, haka kumburi musamman a gwiwa da wasu gaba na nuna halaman bakkale. A tattara duk ire iren su a kai kasuwa. HANA YADUWAN TARI Ciwon tari yana kama dabba da mutum. Halamomin tari basu bayyana a dabba da wuri, don haka duk abun da za'ayi yakan zama a makare. Halamomin tari a shanu sune: Tari Ramewa Matsalar numfashi, sannan a wani sa'in akwai kumburewan wuya. Kasancewar halamomi na bayyana a makare, ba'a iya hana yaduwar tar a dabbobi. Abun farin ciki, bamu samu dabbobi masu ciwon tari sosai a Ladduga ba. Ayi amfani da wadannan hanyoyi don rage ko hana 11 : Disease Brucellosis Bovine tuberculosis Fufulde name Period of sampling Bakale June 2011 Cattle October 2011 Sheep Helminths Bonostomum phlebotomum Cooperia pectinata Oesophagostomum radiatum Strongyloides papillosus Tricuris globulosa Strongylus laryngeus Paramphistomum cervi Fasciola gigantica Eimeria bovis Schistosoma bovis Moniezia benedeni How many animals/ How many HH/ people are infected? herds are infected? 10/1963 = 0.5% 7/40 = 17.5% 2/717 = 0.3% 2/52 = 3.8% Goat 717 (52 752 (52) 0% 0% People 1124 (80) 0% 0% Cattle 1944 (40) 103/1944 = 5.2% 29/40 = 72% June 2011 Cattle 1982 (40) 278/1982 = 14% 34/40 = 85% October 2011 Sheep 717 (52) 31/717 = 4.32% ND2 Goats 752 (52) 24/752 = 3.09% ND June 2011 Trypanosomiasis Samore (overall prevalence, cattle with 1 or more of helminths below) Number animals/ people sampled (no. Hh1 Sampled) 1963 (40) Tari Disease Species Fufulde name Hanta/ Goli Period of sampling Species Number animals/ people sampled (no. Hh1 Sampled) June 2011 Cattle 1981 (40) How many animals/ How many HH/ people are infected? herds are infected? 1332/1981 = 62.2% 39/40 = 97.5% Goli Goli Goli Goli 4/1981 = 0.2% 3/40 = 7.5% 145/1981 = 7.3% 296/1981 = 14.94% 19/40=47.5% 32/40 = 80% Goli Goli Goli Goli Hanta Goli Goli Goli 12/1981= 0.61% 237/1981 = 11.96% 0/1981 = 0% 850/1981 = 42.91% 106/1980 = 5.35% 353/1977 = 17.79% 3/1981 = 0.15% 1/1981=0.05% 4/40 = 10% 16/40 = 40% 0/40 = 0% 39/40=97.5% 25/40= 62.5% 36/40 = 90% 2/40 = 5% 1/40 = 2.5% 4 FADAKARWA DA SHAWARWARI GA MAKIYAYA AKAN SAMMORE, KUDAN TSANDO, GOLI, HANTA, BAKKALE DA KUMA TARI. SAMORE: Sammore ciwo ne wanda cizon kudan tsando ke haddasa wa dabbobi (Shanu, Tumaki, Awaki,e.t.c). Sammore kan iya shafan mutum ma. ciwon na bayyana bayan kwayar ta shiga jinin dabba, tare da hayayyafa. halamomin ciwon a dabba sun hada da zazzabi, tashin gashi, hawaye,ramewa,jemewar gashin wutsiya sannan kuma in yayi tsanani, dabba yayi ta cin kasa har ya mutu. Sammore yafi kama shanu, amman tumaki da awaki ma suna yin Sammore. Binciken da muka yi a Ladduga ya nuna shanu da yawa na fama da Sammore, amma tumaki da awaki basu da wannan damuwar sosai. Don haka, Shanu sun cancanci kariya daga sammore. Sai a ringa yiwa dukkan garken shanu alluran rigakafin Sammore, a kuma kare su daga tsando. Duk da wadannan kariyan, ba'arasa kadan daga cikin shanu masu kamuwa da sammore. In haka ya faru, to sai ayi anfani da magani na musamman don jinya. Tattaunawan da muka yi daku ya nuna kuna yin abinda ya dace a kan sammore, amma shawarin mu 5 - - - shiga. Wannan “Clostridium” shi yake haddasa kisa ga dabban da ke da “hanta”. Ma'aikatar binciken cututtukan dabbobi da ke VOM, wato N.V.R.I na yin maganin rigakafin wannan ciwon Clostridium, an fi sanin wannan magani da HANTAVAC. Don bawa dabbobin mu cikakken kariya sai a ringa ba shanu da tumaki/awaki maganin duri da rigakafin HANTAVAC. Ana yin rigakafin hanta sau biyu a shekara, (Bazara da kaka). BAKKALE DA TARI Bakkale da tari cututtuka ne masu addaban dabbobi da mutane. Alhamdulilahi, anan Ladduga dai bamuga wadannan matsalolin sosai ba. Shanu kadan aka samu da bakkale da tari. Abun murna, ko mutum daya ba'a samu da ciwon bakkale ba. Wannan ya nuna ana kula sosai. Shawarin mu anan kawai shine: (a) A kula sosai kada dan kadan na dabbobi masu matsalan nan su yada wa sauran. (b) Mutane su yi hattara kada su kamu da cuttuttuka (Bakkale da Tari) daga dabbobi marasa lafiya. HANA YADUWAR BAKKALE Wadannan hanyoyin zasu rage yaduwar bakkale sosai. 10 - ga karuwar kuda ko randa za'a shigo inda ke da kuda sosai. Anfi samun tsando kusa da manyan rafuka kamar rafin Kaduna, inda ke da kurmuna da kuma gangare. GOLI DA HANTA Goli da hanta wasu tsutsotsi ne da ake samu a hanji da hantan dabbobi masu matsalar. Shanu, tumaki da awaki duk suna kamuwa da goli ko hanta. Binciken da muka yi a Ladduga ya nuna shanu da yawa na dauke da hanta da goli. Haka kuma tattaunawan mu da mahautan Ladduga, sun gaya mana sukanga wadannan tsutsotsi a hanji da hantan dabbobin da aka yanka. Abun farin ciki anan, akan iya magance goli da hanta da magani daya. Ayi wa dabbobi duri a farkon damina (watan shida) da karshen damina (watan tara). Ayi amfani da magani mai sinadarin Levamisole da Oxyclozanide, misali KEPZAN. Ana bawa babbar sa kwaya daya da rabi zuwa kwaya biyu na Kepzan. Sai a budi bakin sa a sa kwayar magani, a bida ruwa. Kar a sha madaran san da aka bada Kepzan sai bayan kwana daya. Hanta da goli basu kashe dabba, amma kasancewar su a hantan dabba kan yi wa hantan lahani ta inda wata kwayar ciwo nau'in “Clostridium” ke samun 9 anan kawai, a ringa yin wa dukkan garke alluran rigakafin sammore, a tabbatar ana bada dai-dai yawan maganin da ya dace da girman dabba. Shanun da basu da lafiya kuma, ayi amfani da maganin jinya. H A N YA N B A D A S H A N U K A R I YA D A G A SAMMORE: Ayi amfani da Samorin a farkon bazara (watan Biyar zuwa Shida), ko kamin a kaura zuwa wuraren dake da tsando.haka kuma kamin dawowa zuwa Ladduga. A tabbatar an bada magani bisa girman dabba, domin in magani ya kasa, ya kan iya jawowar bijirewar kwayar sammore (resistance). Aguji yin alluran samorin a wuya musamman in Shanun noma ne. Samorin na bada shanu kariya na wata uku, amma a nau'in sammore mai wuyan sha'ani, kariyan baya kai wata uku. YADDA AKE HADA SAMORIN DA KUMA YIN ALLURA: Kayi amfani da ruwan da aka tafasa kuma ya huce wajen hada samorin. Ka gwada ruwa lamba hamsin ko dari wato allura biyar ko goma (50mls, or 100mls), ka juye pakitin samorin mai nauyin giram daya a ciki, ka jijjiga har sai magani ya narke gaba 6 - - Weight of the animal daya. Ka huda samorin cikin tsoka (i/m) in an jika da lamba hamsin ne, a bada babbar sa lamba biyar (5 mls), in kuma da lamba dari aka jika, a bada lamba goma (10 mls) wa babbar sa. In akwai wata dabba mara lafiya kuma ana kyautata zato sammore ne, to sai ita a bata maileda. - 2% Solution 0.6mg/kg - A bada babbar sa lamba goma sha daya zuwa sha uku (11 13mls) bisa ga nauyin ta. Shima maileda ana yin alluran a cikin tsoka(i/m). Kar a sha madarar san da aka mata allura da maileda har sai bayan kwana bakwai (7days). Kar a biye maileda da samorin ko samorin da maileda har sai bayan sati uku. Kar ayi ajiyan hadadden maileda ko samorin, ayi amfani da su da zaran an jika. 1mg/kg 50kg 1.25ml 2.5ml 100kg 2.50ml 5ml 150kg 3.75ml 7.5ml 200kg 5ml 10ml 250kg 6.25ml 12.5ml 300kg 7.50ml 15ml 350kg 8.75ml 17.5ml 400kg 10ml 20ml KARE DABBOBI DAGA CIZON KUDAN TSANDO Binciken da muka yi ya nuna babu tsando sosai a Ladduga, amma lokacin kaura akan iya fada a wuraren da ke da tsando sosai. Akan iya tsere wa sammore in ana kauce wa wadannan wurare. In ya zama tilas a ziyarci wadannan wurare, to ayi amfani da magani na musamman don kariya daga tsando. Magani mai sinadarin Deltamethrin, misali Vectocid na bada shanu kariya sosai. YADDA AKE HADA MAILEDA Kayi amfani da ruwan da aka tafasa kuma ya huce. Ka jika karamin patikin maileda (2.36g) daya da ruwa lamba goma sha biyar (15mls). Ajijjiga har sai magani ya narke gaba daya kamin ayi wa shanu allura. 7 YADDA AKE AMFANI DA VECTOCID Ka zuba lamba daya (1ml) na vectocid a ruwa lita daya, ka garwaya sosai. Kayi amfani da abin feshi na hanu ka fesa wa ko wane sa babba lita daya zuwa uku (13 litres) a wuraren da tsando suka fi cizo/zama a jikin sa kamar karkashin ciki da kafafuwa. Kayi amfani da wannan magani a duk lokacin da ka 8
Similar documents
Chapter 19 - Masjid Tucson
huhunci ne na Ubangijinka. *19:71 Kamar yadda bayanin shafi 11 ta gwada, za tayar da mu kafin ainihin zatin Allah ya bayyana ga kaunin sammarmu. Wannan shi ne zai kasance dandanawar Jahannama na zu...
More information