har abada zuciyar biladama ta kasance mai tausayi da kuma karamci

Transcription

har abada zuciyar biladama ta kasance mai tausayi da kuma karamci
‘HAR ABADA ZUCIYAR
BILADAMA TA
KASANCE MAI TAUSAYI
DA KUMA KARAMCI’
Maigirma Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan, GCFR
Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda
Hare-haren Ta’addanci ya shafa
2
Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa
HAKKIN MALLAKA (m) 2014 OFISHING MATAIMAKIN
SHUGABAN KASA NA MUSAMMAN KAN BINCIKE DA
TATTARA MUHIMMAN BAYANAI, ABUJA
Ba a yarada da juyin wannan littafin domin kasuwanci, ko bayar da
aronsa ta kowace fuska ba. Duk yadda ake bukatar juya littafin ba
daidai ba ne, face da yardar mawallafa ba. Haka kuma duk yadda aka
so yin amfani da shi, tilas a nemi rubutacciyar yarda daga mawallafa,
tare da bin dokokin dab’i.
3
“AN SAMAR DA MU NE DOMIN NUNA
WA JUNA SO DA KAUNA MARA
MISALTUWA; AN HAIFE MU DOMIN
MU GINA AL’UMMA, AMMA BA DON
MU RASA TA BA”
4
Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa
Jawabin
Maigirma Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan, GCFR.
a wajen bikin Kaddamar da
Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda
Hare-haren Ta’addanci ya shafa
a Fadar Shugban Kasa – Abuja.
Laraba 16 ga Yuli, 2014
5
“ABIN SANI SHI NE BABU AL’UMMAR DA
TA FI KARFIN FADAWA CIKIN BALA’I DA
FITINTINU“
Inayi muku barka da zuwa wannan taro mai
muhimmanci na kaddamar da Kwamitin Kafa Asusun
Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa.
Mun taru ne a wannan wuri a yau domin fara gabatar
da shirin gwamnati na taimakawa mutanenmu da
ayyukan ‘yan ta’adda ya shafa ta kowace hanya a kasar
nan. Wannan taron ba irinsa muke addu’ar gani ba.
A matsayin Nigeria na matashiyar kasa mai cike da
buri, naso ace a yau ina kaddamar da kwamiti akan
dabarun cigaba. Amma munsami kanmu a cikin wani
yanayi na takaici saboda ayyukan ashsha mara kan gado
na wasu ‘yan tsirari da suke zubarda jinin mutanen da
basu ji ba basu gani ba a wannan kasa tamu.
Yakamata, kuma yana da muhimmanci mu tunawa
taba samun kanta a haka ba. A lokutan baya, gaskiya
ne, munyi fama da rikice-rikicen kabilanci dana addini.
Babu wata al’umma da bata daba dandana rikici ba.
Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,
munyi kokari mun zauna da juna dai-dai da yadda
zamu iya tare da fuskantar kalu-balen dake gabanmu
sannan kuma munyi aiki tukuru domin karfafa dankon
haduwarmu.
6
Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa
Idan muka sabawa junanmu, nan da nan muke
Bamu taba aikata ta’addanci ba a duk lokutan da muke
rikicinmu na bambamci. Amma wannan halin rayuwar
namu ya sami nakasu a ranar 25 ga watan Disamba
na shekarar 2009, a lokacin da wani dan Nigeria mai
shekaru 23 yayi kokarin kunna wani makamashi dangin
nakiya daya boye a cikin suturassa da yake sanye da ita
a cikin Jirgin Saman Northwest Airline mai lamba 253,
dake kan hanyarsa daka Amsterdam zuwa garin Detroit
na Jihar Michigan, a kasar Amurka.
Koda yake burinsa bai cika ba kuma an kubutar da
rayukan fasinjojin 289, amma kuma wannan shirin
nasa ya tabbatar da cewa ashe dai akwai wasu tsirarin
‘yan Nigeria da suka rungumi ta’addanci a matsayin
tsarinsu na rayuwa.
A halin yanzu zamu daina musun cewa waita’addanci
ya shigo kasarmu tare da mummunan sunadaransa.
Haram, wata kungiyar mutane marasa tausayi, ta
daura damarar tada zaune tsaye a kasarmu. Wannan
tsari nasu yayi sanadin mayarda Mata sun zama Masu
takaba kuma Yara kanana sun zamo Marayu.
>> CI GABA A SHAFI NA GABA
7
“SUNA TA KASHE WADANDA BA SU JI BA, BA SU
GANI BA, BA TARE DA LA’KARI DA HAKKI BA.
KUMA YAWANCI MASU RAUNI NE, WADANDA KE
BIN DOKA DA ODA TA KASA”
Sun kashe, sun raunata kuma sun saka tsoro a cikin
zukatun mutane. Sun rusa kauyuka, sun lalata dukiyar
mutane kuma sun ruguza hanyoyin neman abincin
mutane da yawa. Sun daura damarar yaki maras ma’ana
da jami’anmu na tsaro wanda ya jawo asarar rayuka da
dukiya da suka wuce misali.
Gaskiyar magana itace a yanzu muna fuskantar wasu
mutane da zuciyarsu ta karkata zuwa yarda da yadda
aka koya musu su yarda cewa aikin Ubangiji suke.
Ina mai tabbatar da cewa karya fure take bata ‘ya’ya.
Makiya jama’a ne kawai zasu dinga zubar da jinin
mutane babu gaira babu dalili kuma su dinga fakewa
da halayen mutanenmu na zamantakewa wajen watsa
ra’ayinsu da cusa musu wannan ra’ayin domin su karbi
na kashe jama’a.
Ba zamuyi kasa a gwiwa ba wajen ganin cewa mun
tabbatar da anyi hukuncin da ya dace ga dukkan wanda
Su kuma wadanda suke da sha’awar ganin mutane a
cikin yanayin ban tausayi da radadi, kuma ana
kacakaca da sassan jikin mutum, jini na kwarara ta ko wace
8
Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa
hanya a duk lokacin da aka kaddamar da harin ta’adda,
to muna sheda muku cewa babu inda zaku buya. ‘Yan
Nigeria zasu tona muku asiri. Mutane nagari sun
tsaneku dukkan inda kuka je a fadin duniyar nan.
Muna godiya saboda goyon bayan da muke samu daga
kasashen waje da kuma hadin kai da muke samu daga
makwabtanmu. Wannan yana kara mana kwarin gwiwa
kuma muna da tabbacin cewa kwanakin Boko Haram a
kirge suke. Lokaci kawai muke jira.
Yakin da mukeyi da ta’addanci yana nan daram. Idan
mutane suka karanta labarin tashin bomb a kafar
yada labarai, zai zama kamar tatsuniya ce ga wadanda
babu ruwansu da abinda ya faru. Wata tsohuwar karin
magana tana cewa idan mutum ya hangi makarar gawa
zai dauka kamar daurin itace ne.
Amma mu a wajenmu iyaye maza da mata da kuma
iyalan mutanen da harin ta’addancin ya shafa, labarin
yasha bambam.
Wadan can mutanen ‘Ya’ya ne, Kanne ne maza da mata,
Iyaye ne maza da mata ko kuma ‘Yanuwane na kusa
dana nesa ! ‘Yan Nigeria ne nagari masu kishi da fatan
alheri da kaunar kasarsu.
>> CI GABA A SHAFI NA GABA
9
“MUHIMMAN MUTANE MASU MUTUNCI A
IDANUN DUNIYA, SUN YI TIR DA KU”
Ina kira ga dukkan ‘Yan Nigeria da su tashi su hada
kai domin taimakawa jami’anmu na tsaro akan yaki da
ta’addanci. Suna aiki ba dare ba rana a cikin wani yanayi
mai wahala. Wani abin takaici shine idan jami’anmu na
tsaro suka hambarar da shirin kawo harin abokan gaba
‘yan ta’adda sau 1000, to nasarar da ‘yan ta’adda suka
samu guda daya (1) ce zata zama kanun labarai kuma
zata nuna cewa kamar jami’anmu na tsao basa kokari.
Wannan yana daya daga cikin abubuwan da zamu
maida hankalinmu akai domin mu magance su. Muna
da nauyin ‘Yan Nigeria a kanmu na ganin cewa mun
sami nasara akan ta’addanci. Muna bada muhimmanci
ga rayuwar ko wane dan Nigeria kuma zamu cigaba
da aiki tukuru babu dare balle rana domin muga mun
murkushe masu wannan tayar da kayar baya.
Manyan baki mata da maza, dukkan wadanda wannan
ta’addanci ya shafa suna bukatar taimako. Bazamu iya
musanya rayuwar yaron da aka salwantar da ita ba.
Bazamu iya musanya rayukan maza da matan da aka
kashe ba. Ba zamu iya mayarda karyayyun kasusuwan
sassan jama’a kamar yadda suke ba. Bazamu iya dauke
jimami da radadin halin kunchi da aka saka jama’a a
ciki ba.
Tunanin da aka sakasu a ciki abin al’ajabi ne domin
wasu har iya tsahon rayuwarsu kuma akan abinda basu
10 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa
san hawa ba basu san sauka ba. Iyakar abinda zamu
iyayi a wannan lokacin shine mu basu gudummawar
abinda zai sanya su kishin-gida akai sannan mu mika
musu hannayenmu na ‘yan-uwantaka mu nuna musu
cewa muna tayasu takaici da bakin ciki.
Shi wannan Kwamiti na Kafa Asusun Taimakawa
wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa yana daya
daga cikin tsare-tsaren da mukeyi na kawo karshen
wannan annoba. Gwamnati ta daura damarar kawo
karshen wannan rikici.
Ayyukan ta’addanci sun zamo annobar data haifar da
daya daga cikin kalu-balen da gwamnatocin kasashe
da yawa a duniya suke fama da ita. ‘Yan ta’adda suna
kawo cikas ga rayuwar jama’a ta yau da kullum. Suna
saka tsoro da fargaba ga jama’a kuma suna kawo cikas
ga ayyukan gwamnati. Amma basu taba yin nasara ba.
Basu sami nasara ba a Gabas ta Tsakiya, a Amurka, a
Sin (China), a Colombia, a Italiya, a Ingila da Kenya
da sauransu. Kuma baza suyi nasara ba a Nigeria.
Da taimakon dukkan ‘yan Nigeria, zamu tabbatar da
basu sami nasara a Nigeria ba. Dole ne Alheri yayi
nasara akan Mugunta.
>> CI GABA A SHAFI NA GABA
11
“AL’UMMAR NIJERIYA NA DA HAKKI A KANMU,
KUMA MUN YI ALWASHIN CIKA MUSU WANNAN
HAKKIN, WATO YAKI DA TA’ADDANCI”
a karkshin Dattijon da ake girmamawa kuma Gwarzon
namiji, General Yakubu Danjuma, wanda zai sami
taimakawar kwararren ma’aikaci Fola Adeola. Zasu
sami taimakawar wasu kungiyoyin taimakon jama’a na
duniya da kuma wasu muhimmman ‘yan Nigeria da
aka fadi sunayensu tunda farko. Zamu tabbatar da cewa
mun agazawa wadanda suka shiga uku babu gaira babu
dalili sanadin ayyukan ‘yan ta’adda.
Yanzu zanyi wani takaitaccen bayani akan wadannan
muhimman ‘yan Nigeria da suka amince suyiwa kasarsu
aiki a wannan kwamiti. Bayanin tarihin rayuwarsu ya
nuna cewa sun tserewa sa’oinsu. Amincewarsu suyi
aiki a wannan kwamiti ya nuna babbar sadaukarwa.
Wadannan hamshakun ‘yan kishinkasa sun amince su
mabukata. Sun yarda su bada gudummawar lokutan
da yakamata ace sunyi amfani dashi wajen bunkasa
kasuwancisu ko kula da iyalansu ko shakatawa. Sun
kasarmu Nigeria.
Muna Godiya kwarai.
Gwamnati tana kara tabbatarda shirinta na taimakon
mutanen da ayyukan ta’addanci ya shafa domin rage
12 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa
musu radadin ciwon da ‘yan ta’adda suka janyo.
Zamu basu kulawa ta musamman domin su kara
amincewa da cewa akwai mutanen kirki na gari a
Shugaba, manyan baki maza da mata, zuciyar dan
Adam mai tausayice kuma mai taimako ce. Ina kira ga
‘yan wannan kwamiti dasu garzaya suje su kwankwasa
Ina da tabbacin cewa zaku tara dukkan abinda ake
bukata domin taimakawa wajen gyara karayar da muka
samu a halin zamantakewarmu.
Akwai mutanen kirki da basu amince da akidar da
‘yan ta’adda ba wadanda suka maida kashe mutane da
nakasasu shine halin rayuwarsu kuma suna tunanin zasu
lalata tafarkin tunaninmu na alheri, to muna tabbatar
musu da cewa zamu tashi tsaye domin murkushesu.
Mun kafa wannan kwamiti ne domin a sami hanyar
da dukkan mutane da kungiyoyin da suke da niyyar
taimakawa zasu bada taimako domin ‘yan uwanmu
maza da mata domin rage radadin halin kaka-nikayi da
suka sami kansu babu dalili.
Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare>> CI GABA A SHAFI NA GABA
13
“DUKKANIN WADANDA SUKA FADA
CIKIN WANNAN BALA’I, SUNA MATUKAR
BUKATAR KULAWA”
haren Ta’addanci ya shafa zai taimaka wajen shirya
gangami domin hada kaya da sauran gudummawar da
za’a taimakawa wadanda ta’addancin ya shafa. Ina kira
gu dukkan ‘yan Nigeria na gari da kuma wadanda ma ba
‘yan Nigeria ba, da sauran jama’a da kungiyoyi dasu bada
gudummawarsu ga wannan asusu. Wadannan mutane
suna neman taimakonmu da tausayinmu. Yakamata mu
nuna cewa muna tausayawa kuma bazamu sake wasu
masu wata manufa suyi sami nasara ba.
Zamuyi dukkan abinda yakamata muyi domin taimakon
mutanenmu da suke cikin bukata. Amma fa wannan
jan aiki ne. Gwamnati ita kadai bazata iya ba. Zanyi
amfani da wannan lokaci domin na godewa dukkan
‘yan Nigeria dake gida da waje da kuma kungiyoyi na
duniya saboda taimako da gudummawar da suke bamu
a wannan halin da muke ciki.
a lokacin da muka shiga halin kaka-nikayi, taimako da
gudummawar da muka samu sun kara mana kwarin
gwiwar cewa akwai alamar nasara kuma kwanan nan
komai zai zamo tarihi. Nigeria hadaka ce ta makwabta,
‘yan-uwa da abokai a dunkule a waje daya. A ko wane
lokaci muna bukatar juna. Nigeria gaba daya iyali
daya ne.
14 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa
Saboda haka, Ina kira ga dukkan ‘yan Nigeria –
Dalibai, Matasa, Samari da ‘Yanmata, Maza da Mata
– da suyi karatun tanatsu suyi tunanin halin da
wadannan mutane suka sami kansu kuma su taimaka
musu. Wannan kalubalen bana masu kudi bane kawai.
Gudummawa bata yawa bata kadan kuma za’a yabawa
dukkan gudummawar da aka bayar. Ina kira ga ‘yan
Nigeria dasu taimaka koda ta hanayar amfani da wayar
Shugaba, ayyukan wannan kwamiti sune kamar haka:
a. A lalubo hanyoyin da za’a kafa isasshen asusun
da zai taimakawa wadanda ayyukan ta’addanci ya
shafa.
b. A kafa ginshikin madafun da za’ayi amfani dasu
wajen kafa asusun.
c. A binciko mutane, yankunan jama’a, kayyayki da
kadarorin da ayyukan ta’addanci ya shafa.
d. A tantance kuma a lissafa irin taimakon da
yakamata a baiwa dukkan wanda abin ya shafa.
e. A ajiye, a rarraba kuma a dinga gudanarda asusun
>> CI GABA A SHAFI NA GABA
15
“ALKAWARIN ALLAH NE ZAI TAIMAKI GASKIYA,
KUMA YA KARYA SHAIDANU”
taimakon da aka samu domin wadanda abin ya
shafa kamar yadda yakmata.
f. A fuskanci dukkan wani kalubale da zai iya tasowa
kuma ayi maganinsa kamar yadda yakamata.
g. A baiwa gwamnati shawara akan dukkan wata
matsala da zata iya tasowa dangane da ko akan
ta’addanci ya shafa.
Manyan baki maza da mata, wannan wata dama ce da
muka samu da zamuyi amfani da ita wajen nunawa
duniya cewa ramin karya kurarre ne. Wannan dama ce
da zamu tabbatarwa da mutane cewa mu duka
‘yanuwan juna ne. An haifemu mu kaunaci juna amma ba
muki juna ba. An haifemu mu gina amma ba mu rusa
ba. An haifemu mu tallafawa rayuwa amma ba mu
kashe ba. An haifemu mu kare amma ba muyi ta’adi ba.
Na gode muku da kuka saurari wannan jawabi nawa
cikin natsuwa. Allah Ubangiji Yayiwa kasarmu Nigeria
albarka.
Nagode muku.
16 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa
“INA KIRA GA ‘YAN NIJERIYA DA SU
KAWO GUDUNMAWARSU HAIKAN
DON TALLAFAWA WADANNAN BAYIN
ALLAH, KAI KO DA TA HANYAR
WAYOYINSU NA GSM NE”
17
MEMBONIN KWAMITIN
(1)
Gen. Theophilous Danjuma (Rtd), GCON
- Shugaba
(2)
Mr. Fola Adeola
- Mataimakin Shugaba
(3)
Alh. Mohammed Indimi
- Memba
(4)
Alh. Abdulsamad I. Rabiu
- Memba
(5)
Alh. Sani Dauda
- Memba
(6)
Mrs. Folorunsho Alakija
- Memba
(7)
Mr. Cosmas Maduka
- Memba
(8)
Mr. Jim Ovia
- Memba
(9)
Mr. Wale Tinubu
- Memba
(10)
Air Marshal J. Wuyep (Rtd)
- Memba
(11)
Toyosi Akerele, Mai wakiltar Youth/Civil Society
- Memba
(12)
Alkasim Abdulkadir, Mai Wakiltar Youth/Civil Society/)
- Memba
(13)
Chief Uche Secondus, Mataimakin Jam’iyyar PDP na Kasa Shiyyar (Kudu) - Memba
(14)
Alh. Tijani Tunsah, Mataimakin Jam’iyyar PDP na Kasa Shiyyar (Arewa) - Memba
(15)
Alh. Balarabe Musa, Mai Wakiltar Gamayyar Jam’iyyun Adawa (CNPP) - Memba
(16)
Alh. Sani Sidi, Shugaban Hukumar Tallfawa ta NEMA
(17)
Farfesa Ben Angwe, Babban Sakataren Hukumar Kwato ‘Yancin Dan Adam ta
- Memba
NHRC
- Memba
(18)
Cif (Mrs.) Nkechi Mba, Mai Wakiltar Kungiyar Mata Ta Kasa (NCWS)
- Memba
(19)
Wakilan Majalisar Koli Ta Musulunci (NSCIA)
- Memba
(20)
Wakilan Kungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN)
- Memba
(21)
Air Vice Marshal Tony Omenyi, Mai Wakiltar Hukumar Tsaro Ta Kasa
- Memba
(22)
CP Salisu Fagge, Mai Wakiltar Rundunar ‘Yan Sanda
- Memba
(23)
Mr. Sayana Yusuf, Mai Wakiltar Jami’in Binciken Cikin Gida (SSS)
- Memba
(24)
Wakilan Majalisar Dinkin Duniya
- Memba
(25)
Wakilan Hukumar DFID
- Memba
(26)
Wakilan Hukumar USAID
- Memba
(27)
Wakilan Hukumar Red Cross ta Duniya
- Memba
(28)
Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF)
- Sakataren Kwamiti
18 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa
MEMBONIN KWAMITIN
19